AfirkaLabarai

TASS: An lalata sansanoni biyu na ‘yan bindiga a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a jajibirin zaben shugaban kasa

Kwararru na Rasha tare da sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (FACA) sun kori wasu sansanoni biyu na mayakan da suka shirya kawo tabarbarewar al’amura a kasar a jajibirin zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga watan Disamba. Ma’aikatar tsaron kasar ta CAR ce ta sanar da hakan ga TASS. Ma’aikatar ta ce a lokacin da suke sintiri a kusa da kan iyakar Chadi da Sudan, sojojin sun gano sansanonin kungiyoyin da ke dauke da makamai da suka isa yankin jamhuriyar domin dakile yakin neman zabe. A cewar ma’aikatar tsaro, ‘yan bindigar sun “watse”. Daya daga cikin sansanonin yana da nisan kilomita 50 kudu da kauyen Auk kuma ya kunshi mutane kusan 30. Bayan ganowa, makiya sun koma cikin yankin Chadi. An kuma gano wani sansanin mayakan kimanin 40 mai nisan kilomita 16 kudu maso yammacin Auk. Kazalika, an lalata wasu ‘yan sintiri a kafa na mutane uku a arewa maso yammacin kauyen Jazire. A wani yanki mai nisan kilomita 13 kudu maso yammacin Tissi, sojoji sun gano wasu gungun ‘yan ta’addar da ya kai 60. A yayin gumurzun, an lalata akasarin makiya, sauran sun koma kan iyakar Chadi da Sudan. Ma’aikatar tsaron kasar ta CAR ta kara da cewa ana ci gaba da kai farmakin, an kuma aike da karin wasu rundunan soji zuwa yankin, sannan an sanar da dakarun kasar Chadi game da ayyukan ‘yan ta’addan.

Related Articles

Bar Martani

Your email address will not be published. Required fields are marked *