Ba a biya su alawus-alawus: Super Eagles sun yi barazanar kauracewa wasan daf da na kusa da na karshe na AFCON da Algeria

Super Eagles ta Najeriya sun dauki hoton tawagarsu kafin wasansu da Uganda a gasar cin kofin Afrika. Hoto: NFF Media
Kungiyar Super Eagles ta yi barazanar kauracewa wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Nahiyar Afrika (AFCON) da za ta yi da Algeria a birnin Marrakech muddin hukumar kwallon kafa ta Najeriya ba ta daidaita batun biyan alawus-alawus ba.
Wata majiya a cikin ‘yan wasan ta tabbatar da cewa ‘yan wasa da jami’ai na ci gaba da jiran alawus-alawus daga gasar da suka hada da samun nasara a wasan da suka yi da Tanzania da Tunisia da Uganda da kuma Mozambique.
Majiyar ta bayyana cewa, yayin da kungiyar ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da gasar, sun bayyana karara cewa ba za su yi atisaye ba, ba za su yi tattaki ba har sai an warware matsalar.
Wannan dai ya biyo bayan takaddama makamanciyar wannan ne a watan Nuwamba lokacin da ‘yan wasan suka yi barazanar kauracewa wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da kasar Gabon saboda rashin biyansu hakkokinsu.
A lokacin, ‘yan wasan da ma’aikatansu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka ce, “’Yan wasan da suka hada da jami’ai, sun hana su atisaye a yau a kasar Morocco saboda matsalolin da ba a warware su ba tare da rashin biyansu albashi, Super Eagles na jiran matakin gaggawa na ci gaba da shirye-shiryen wasan da za su yi da Gabon ranar Alhamis.”
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta mayar da martani inda ta bayyana cewa babban bankin Najeriya CBN na sarrafa alawus-alawus ga wasu bankuna.
Dan jarida Tobi Adepoju ya ruwaito a ranar Laraba cewa ya tattauna da wani jami’in hukumar ta NFF inda ya ce, “An fara sarrafa kudaden ne daga CBN zuwa bankuna daya, ‘yan wasa da jami’ai za su karbi dukkan alawus din su idan an kammala aikin.
Wani dan jarida, Oluwashina Okeleji, ya tabbatar da matsayin ’yan wasan, inda ya rubuta cewa, “har yanzu ba a samu lamunin nasara a wasanni hudu da suka yi da Tanzania, Tunisia, Uganda da Mozambique ba. Kungiyar ta ci gaba da maida hankali, amma ‘yan wasan ba za su yi atisaye ko tafiya zuwa Marrakech a ranar Alhamis ba idan ba a magance hakan ba.
Najeriya ta samu nasara a dukkan wasanni hudu da ta buga a gasar kawo yanzu, inda ta doke Tanzaniya da ci 2-1, Tunisia 3-2, Uganda 3-1 da Mozambique 4-0 a zagaye na 16. Tawagar da Eric Chelle ke jagoranta, za ta kara da Algeria a ranar Asabar 10 ga watan Janairu, inda za ta je wasan kusa da na karshe.



