Wasanni

Mbappe bai halarci atisaye ba yayin da Arbeloa ke jagorantar Real Madrid

Mbappe bai halarci atisaye ba yayin da Arbeloa ke jagorantar Real Madrid

Mbappe bai halarci atisaye ba yayin da Arbeloa ke jagorantar Real Madrid

Dan wasan gaba Kylian Mbappe ba ya nan ne yayin da kociyan Real Madrid Alvaro Arbeloa ya jagoranci atisayensa na farko a ranar Talata, bayan ya maye gurbin Xabi Alonso a jagorancin kungiyar ta Spaniya.

An nada Arbeloa ne a ranar Litinin kuma wasansa na farko zai kara da Albacete a gasar Copa del Rey ranar Laraba, wanda da wuya dan wasan Faransa Mbappe zai buga.

Mbappe ya dawo daga jinyar da ya yi a gwiwarsa a lokacin da ya maye gurbinsa a wasan karshe na cin kofin Spanish Super Cup da Barcelona ta doke su a ranar Lahadi, amma da alama zai ci gaba da kokarin ganin ya murmure har zuwa wasan da za su yi da tsohuwar kungiyarsa ta Monaco ranar Talata mai zuwa.

Majiyar Real Madrid ya shaida wa AFP cewa “yana da ma’ana” Mbappe bai halarci atisaye ba, saboda matsalar gwiwarsa.
Tsohon kociyan kungiyar, Alonso, ya amince cewa akwai hadari a hada dan wasan da ya zura kwallaye a raga a karawar da suka yi da Barca a Saudi Arabia.

Alonso, wanda aka maye gurbinsa da shi bayan bai wuce watanni takwas ba yana jan ragamar kungiyar, ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa zai bar kungiyar, saboda ya yi iya kokarinsa.

“Abubuwa ba su tafi kamar yadda nake so ba,” kocin Basque ya rubuta a Instagram ranar Talata.

Kocin Real Madrid abin alfahari ne kuma nauyi ne, Ina godiya ga kungiyar, ‘yan wasa, da sama da duk magoya bayanta saboda kwarin gwiwa da goyon bayansu.

“Na tafi cikin girmamawa, tare da godiya, da kuma girman kai na yin iya ƙoƙarina.”

Related Articles

Bar Martani

Your email address will not be published. Required fields are marked *