Wasanni

Osimhen ya isa birnin Alkahira yayin da Super Eagles ta tashi zuwa Fes

Osimhen ya isa birnin Alkahira yayin da Super Eagles ta tashi zuwa Fes

Dan wasan Galatasary, Victor Osimhen shi ne dan wasa na karshe da ya zo a sansanin ‘yan wasan Super Eagles a jiya daf da tashi da tawagar kasar zuwa birnin Fez na kasar Morocco, inda za su buga wasannin rukuni-rukuni a gasar cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2025.
 
Najeriya za ta buga wasanta na farko na gasar da kasar Tanzania a ranar 23 ga watan Disamba, kwanaki biyu bayan da aka fara gasar a duk shekara.
 
Super Eagles da suka yi sansani a birnin Alkahira daga ranar Asabar zuwa jiya, sun buga wasan sada zumunci da Fir’auna na Masar, inda suka yi rashin nasara da ci 1-2.
 
Dukkanin ‘yan wasa 28 da aka zaba a gasar sun shiga atisayen da kungiyar ta yi a safiyar jiya a Masar, sai dai Osimhen, wanda ake sa ran nan gaba a ranar.
 
A cewar Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, ana sa ran Osimhen zai kasance cikin shirin da za a yi na maraice da karfe 5.00 na yammacin jiya.
 
Samuel Chukwueze da Moses Simon, wadanda suka isa sansanin kungiyar da sanyin safiyar jiya, sun bi sahun sauran a atisayen da suka yi da safe.
 
Daga cikin ‘yan wasan da ke wakiltar Najeriya a gasar akwai masu tsaron gida Francis Uzoho da Stanley Nwabali da kuma Amas Obasogie. Sauran sun hada da Ebenezer Akinsanmiro, Fisayo Dele-Bashiru, Semi Ajayi, Ademola Lookman, Bright Osayi-Samuel, Igoh Ogbu, Tochukwu Nnadi, Zaidu Sanusi, Paul Onuachu, Frank Onyeka, Calvin Bassey da kuma Alex Iwobi.
 
Haka kuma a cikin tawagar akwai Wilfred Ndidi da Bruno Onyemaechi da Cyriel Dessers da Akor Adams da Chidera Ejuke da Raphael Onyedika da Ryan Alebiosu da Salim Fago da Chidozie Awaziem da Usman Muhammed da Moses Simon da Samuel Chukwueze da kuma Victor Osimhen.
   
Hukumar ta NFF ta ce Super Eagles za ta tashi zuwa Fés ne a cikin jirgin hayar da za su fafata da Tanzania da Tunisia da Uganda a rukunin C, yayin da Fir’auna za su je Agadir domin buga gasar rukunin B da Afirka ta Kudu da Angola da kuma Zimbabwe.

Related Articles

Bar Martani

Your email address will not be published. Required fields are marked *