Wasanni

Kotu ta daure tsohon dan wasan Premier da laifin zamba a jarabawa

Kotu ta daure tsohon dan wasan Premier da laifin zamba a jarabawa

Rahotanni sun bayyana cewa an tasa keyar tsohon dan kwallon Premier Ramadan Sobhi gidan yari bayan samunsa da laifin zamba a kasar Masar, inji rahoton express.co.uk. Dan wasan mai shekaru 28, ya buga wasanni 45 a gasar Premier a lokacin da Stoke City da Huddersfield Town.
 
Sobhi ya koma Ingila ne a shekarar 2016 bayan ya koma Stoke daga Ahly SC. Dan wasan wanda ya rika buga wasa tare da dan wasan Liverpool Mohamed Salah a wasannin kasa da kasa a Masar, ya buga wa Potters wasanni 46 kafin ya koma Huddersfield a shekarar 2018 gabanin kakar wasa ta biyu ta Terriers a gasar Premier da ta kare.
 
Koyaya, ya buga wa kulob din Yorkshire wasa sau hudu kawai kafin ya koma kasarsa don shiga Pyramids FC a yarjejeniyar dindindin a watan Satumba 2020.
 
A cewar De Telegraaf, an kama Sobhi ne a watan Yuli bayan zargin karya takardun hukuma da sanya wani mutum ya yi jarrabawa a madadinsa a wata cibiyar yawon bude ido da karbar baki. An gudanar da jarabawar ne a gundumar Giza dake tsakiyar kasar Masar.
 
Rahoton ya ce an yanke wa Sobhi da wanda ake kara na biyu hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari tare da aiki tukuru a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Giza ranar Talata.
 
Lauyan Sobhi bai samu damar yin tsokaci ba jim kadan bayan yanke hukuncin, amma yana iya kaddamar da daukaka kara.
  
Sobhi ya fara buga gasar Premier a watan Agustan 2016 lokacin da ya fito daga benci a minti biyu na karshe na wasan da Stoke ta doke Manchester City da ci 4-1.
  
Bayan ya kammala komawa Huddersfield, Sobhi ya samu rauni a gwiwarsa wanda hakan ya sa ba zai taka leda ba na tsawon watanni biyu. Ya buga wasan kwallon kafa na Premier na mintuna 75 kacal ga Terriers kafin ya koma Ahly SC aro a farkon 2019. A karshe ya bar filin wasa na Accu na dindindin watanni 20 bayan haka.

Related Articles

Bar Martani

Your email address will not be published. Required fields are marked *