Wadanda suka ji rauni sun bar sansanin Super Eagles

HARRISON, NEW JERSEY – JUNE 02: Cyriel Dessers #9 (L) da Terem Moffi #19 na Najeriya sun yi dariya kafin wasan da Ecuador a Red Bull Arena a ranar 02 ga Yuni, 2022 a Harrison, New Jersey. Tim Nwachukwu/Getty Images/AFP (Hoto daga Tim Nwachukwu / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / Getty Images ta hanyar AFP)
Kungiyar Super Eagles ta kara kaimi a shirye-shiryenta na tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka zagaye na 16, inda suka yi atisayen da yammacin ranar Juma’a da suka hada da ‘yan wasa 25. Cyriel Dessers ba ya nan ne bayan ya samu rauni a cinyarsa wanda hakan ya tilasta masa barin sansanin ya koma kulob dinsa don jinya.
Ryan Alebiosu ya kasance a wurin amma bai shiga ba yayin da yake ci gaba da murmurewa daga rauni a kafa, yayin da Tochukwu Nnadi shi ma ya zauna a waje saboda rashin lafiya, yana fama da mura.
Babu wani sabon damuwa game da rauni ga ƙungiyar, tare da manyan ƴan wasa duk sun shiga. Victor Osimhen ya yi atisaye ne tare da Ademola Lookman, wanda tuni ya zura kwallaye biyu a gasar, da kuma Raphael Onyedika. Mai tsaron raga Stanley Nubali ka iya komawa fagen wasa bayan an huta da shi a wasan karshe na rukuni da Uganda.
Alex Iwobi, Samuel Chukwueze, Charles Bassey da wasu da dama suma sun shiga cikin zaman gabanin fafatawar da za ta yi da Black Mambas na Mozambique a ranar Talata.
Babban kociyan kungiyar Eric Chelle ya tunatar da ‘yan wasan kungiyar cewa nasarorin da aka samu a matakin rukuni a yanzu sun kasance a baya, inda ya bukace su da su mayar da hankali sosai kan kalubalen da ake fuskanta a zagaye na gaba domin suna da burin ci gaba a gasar.



